Gwamna El-Rufa'i ya koka da kashe mutane a Kaduna
An wallafa
Gwamnan Kaduna ya yi kira da aka kafa wata Babbar Cibiyar Ayyukan Soja (wato Theater Command) kan yaƙi da 'yan fashin daji a yankin arewa maso yamma, kamar yadda ake da mai yaƙi da Boko Haram a Maiduguri.
Malam Nasir El-rufa'i na wannan kira ne jim kaɗan da karɓar rahoton tsaro na shekarar da ta wuce jihar sa ta Kaduna.
Gwamnan ya koka da cewa a bara kawai an kashe mutum 1,129, tare da sace shanu kimanin dubu 13, yayin da adadin mutanen aka sace ya kai ƙiyasin mutum 9 a kullum.
Ya ce masifar garkuwa da mutane da kashe-kashe karuwa yake ba raguwa ba, kuma babu tabbas wannan yanayi na sake daga musu hankali.