Alhaji Aliyu Ibrahim: Za mu faɗa wa gwamnati gaskiya idan ta kama
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ranar Asabar 29 ga watan Janairu ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim sandar girma.
An nada mai martaba Alhaji Aliyu Ibrahim ne a watan Satumban 2021 bayan rasuwar mahaifinsa Sarkin Gaya marigayi Ibrahim Abdulkadir.
To shin ko mene ne sabon sarkin ya sanya a gaba domin ganin cigaban masarautar tasa?
Tambayar kenan da Khalipha Dokaji ya yi masa. To sai dai ya fara ne da bayani kan yadda ya ji bayan an nada shi a matsayin Sarkin na Gaya.