Matashiyar da ke hankoron magance matsalar karancin gidaje

Bayanan bidiyo, Matashiyar da ke hankoron magance matsalar karancin gidaje
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Perala Mansa, wata 'yar kasar Indiya ta kera gida mai suna "O-Pods" wanda za a iya matsawa da shi daga wuri zuwa wuri kuma ba ya bukatar fili mai yawa ko kayan aiki kafin a kera shi.

Matashiyar mai shekara 23 'yar asalin jihar Telangana ta yi amanar cewa gidan wanda ba a kashe kudi da yawa wajen kera shi ba ta hanyar amfani da bututan magudanan ruwa, zai iya magance matsalar karancin gidaje a duniya.

Ta kera gidanta na farko a watan Afrilun 2021.

Yanzu kamfaninta ya yi ikirarin samun kamfanoni da gidajen gona da kuma masu harkar gina gidaje a fadin Indiya da suka kai 500 da ke so a kera musu irin wadannan gidajen.