Yariman Bakura: Abin da ya sa zan tsaya takarar shugaban kasa a 2023
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Senata Ahmed Sani Yarima ya sake ayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben badi.
Senata Yarima wanda tun a shekara ta 2007 ya fara fitowa takarar shugabancin kasar ya yi watsi da tsarin karba-karba a zaman abin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar duk da cewar ana ganin lokaci ne da ya kamata yankin kudancin kasar ya fitar Shugaban kasa na gaba.
Ya bayyana wa BBC Hausa dalilansa na nace wa kan neman shugababancin kasar da kuma matsayinsa game da rikicin shugabancin da jam’iyyar tasa ke fama da shi a jiharsa ta zamfara.
Kalli wani bidiyon na Yariman Bakura: