'Na gaji da dariya da wulakancin da mutane ke min don ni wada ne'
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Will Perry, wani mai ninƙaya da ya wakilci Birtaniya a Gasar Masu Lalura ta Musamman, ya ce "ya gaji matuƙa" kan yadda ake masa dariya da tsokanarsa don kawai shi wada ne.
Ya ce ana damun masu irin halittarsa da tsokana da yi musu dariya a duk inda suka shiga.
Mutumin mai shekara 21 ya yi kira ga mutane da su ƙalubalanci duk masu yin irin hakan.