...Daga Bakin Mai Ita tare da Kabiru Nakwango
An wallafa
Ku latsa hoton sama domin kallon bidiyon:
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 82, shirin ya tattauna da fitaccen dan wasan Hausa mai suna Malam Kabiru Nakwango.
A cikin hirar, Kabiru Nakwango ya yi mana bayani game da rayuwarsa.
Ya kuma shaida wa BBC cewa ya dan daina fitowa a fina-finai ne saboda ya koma harkar koyarwa da kuma noma ka'in da na'in.
Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh
Ɗaukar bidiyo/Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir