Bidiyon Ku San Malamanku tare da Shiekh Tijjani Bala Kalarawi

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Shiekh Tijjani Bala Kalarrawi
An wallafa

Latsa hoton da ke sama ku kalli bidiyon:

Fitaccen malamin addini Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawi ya ce gwagwarmayar neman ilimi ta haɗa shi da manyan malaman ɓangarorin Musulunci a Najeriya Shiekh Abubakar Mahmud Gumi da kuma Dahiru Usman Bauchi.

Shehin malamin ya faɗa wa BBC Hausa haka ne ta cikin Kusan Malamanku, inda ya ce ya san 'yan boko da sarakuna sanadiyyar Abubakar Gumi yayin da ya san manyan malamai a wajen Sheikh Isiyaka Rabi'u da Mahmudu Salga.

An haifi Shiekh Tijjani Bala a shekarar 1947 (shekara 75) a unguwar Fagge da ke Jihar Kano.

Malamin ya shafe mafi yawan rayuwarsa ta zama da karatu a Kano.