Garba Shehu: Mun kusa kawo karshen 'yan fashin daji
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsu ta kusa kawo karshen matsalar 'yan fashin daji.
Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa matakin da gwamnatinsu ta dauka na ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda zai ba su damar tunkararsu gadan-gadan.