Alhaji Shehu Shagari: Abin da ba ku sani ba game da tsohon shugaban Najeriya
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari mutum ne da "ba ka iya juya shi yadda kake so" a lokacin da ya yi shugabancin kasar.
Dansa, Alhaji Muhammad Bala Shagari ne ya bayyana wa BBC hakan a wata hira ta musamman domin cikar tsohon shugaban kasar shekara uku da rasuwa.
Alhaji Shehu Shagari, wanda ya rike sarautar Turakin Sokoto, ya jagoranci Najeriya daga 1979 zuwa 1983 lokacin da sojoji suka yi masa juyin mulki.
Ya rasu ranar 28 ga watan Disambar 2018 yana da shekara 93.
A lokacin da yake mulki, wasu na ganinsa a matsayin mutum mai rauni da ake iya juyawa.
Sai dai Alhaji Bala Shagari ya ce wanda yake wancan tunani "bai san Turaki ba, jinsa yake; su wadanda suka yi aiki da shi sun san ba gaskiya ba ne, don sun san cewa ba haka nan yake ba."
Ya kuma bayyana cewa yana birnin Jos na jihar Filato lokacin da aka yi wa mahaifinsa juyin mulki, yana mai cewa hakan bai dame shi domin ya san cewa mahaifinsa mutumin kirki ne.