Matashiyar da ke shirya taskar waƙoƙin Afirka zuwa intanet
An wallafa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Wata matashiya tana aikin shirya taskar waƙoƙin Afirka tun daga shekarun 1980 zuwa intanet don kada su ɓace ga masu tasowa.
Binetou Sylla tana son gadon mahaifinta wanda ya tattara waƙoƙi da dama na nahiyar Afirka.
Taskar mahaifinta na wakoƙi na da ɗaya daga cikin mafi girma na waƙoƙin Afirka a duniya wanda har ya zuwa yanzu ana samunsu ne kawai a CD.
Binetou na son wannan da aka manta ya zama makomar mawaƙan hip-hop na Afirka.