...Daga Bakin Mai Ita tare da Ado Ahmad Gidan Dabino
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 77, shirin ya tattauna da fitaccen furuduso, darakta kuma mai fitowa a fina-finai wato Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino.
Ado Ahmad, wanda fitaccen marubucin littatafai ne ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da harkokin fim da rubutu.
A cikin hirar ta shaida mana cewa ya samu du,bin nasarori sakamakon rubutu da fim, inda ya zahaya ƙasashen duniya da dama.
Ya rubuta littattafai irin su Inda So da Kauna da Masoyan Zamani da sauransu, waɗanda wasu har an mayar da su na Turanci.
Kazalika an karanta littattafansa a wasu jami’o’i a Birtaniya da Amurka, kamar yadda ya shaida wa BBC
Sannan ya yi fina-finai kamar su Inda So da Kauna din da Juyin Sarauta, wanda ya samu kyaututtukan yabo da dama.
A yanzu haka kuma fuskarsa ta mamaye talabajin a shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in da yake fitowa a ciki a tashar Arewa24.
A cikin shirin ya taka rawar Malam Adamu ne wato gwamnan Jihar Alfawa, inda ya kasance mai gaskiya da son wanzar da adalci.
Amma ya gaya wa BBC cewa wannan fitowa ba ta ya zama mai sha’awar siyasa ba a zahiri kwata-kwata.
Gwamnatin Najeriya ta bai wa Ado Ahmad lambar girmamawa ta ƙasa ta MON.
Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh
Daukar bidiyo da tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir