...Daga Bakin Mai Ita tare da Hauwa Garba, Sabirar Gidan Badamasi

Bayanan bidiyo, ...Daga Bakin Mai Ita tare Hauwa Garba, Sabirar Gidan Badamasi
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 76, shirin ya tattauna da ƴar fim Hauwa Garba wacce aka fi sani da 'Yar Auta ko Sabirar Gidan Badamasi, inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta da fina-finai.

A cikin hirar ta shaida mana cewa ta taɓa auren marigayi Rabilu Musa Ibro har ma sun haifi ɗa sai dai ɗan ya rasu.

Sannan a yanzu tana da ƴa budurwa da take shirin fara fitowa a fina-finai.

Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh

Daukar bidiyo da tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir