Gwarazan ƴan takarar wasanni na BBC Aspoty 2021: Bayani kan Christine Mboma
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An sanar da sunayen waɗanda ke takarar kyautar gwarazan 'yan wasan Afirka na BBC na 2021.
Gudun da na fi so a rayuwata" - haka Christine Mboma ta kwatanta gudun da ta yi a gasar Olympics ta Tokyo da aka yi a 2020 a lokacin da ta zama mace ta farko ƴar ƙasar Namibia da ta tsaya kan dandamalin Olympic.
Nasarar da ta samu ta samun kyautar bayan shekara 25, matashiyar ta lashe azurfa a gudun mita 20, inda ta zo ta biyu bayan ƴar ƙasar Jamaica wadda ta lashe gasar Olympic sau biyar, wato Elaine Thompson-Herah.
Mbomaa ta kammala a cikin daƙiƙa 21.81 wadda ita ce mace ta farko yar ƙasa da shekara 20 da ta taɓa gamawa a cikin wannan ƙanƙanin lokacin.