Gwarazan ƴan takarar wasanni na BBC Aspoty 2021: Bayani kan Ntando Mahlangu
An wallafa
Ku latsa sama don kallon bidiyon:
Ntando Mahlangu ya samu kyautarsa ta farko a gasar nakasassu a lokacin da yake da shekara 14, ya samu kyautar azurfa a gasar nakasassu a gudun mita 200 a wasan da aka yi a Rio a 2016 - shekara biyu bayan da ya soma wasan.
A shekarar, ya ƙara samun kyauta inda ya samu gwal a duka gudun maza na mita 200 da kuma tsallen baɗake a Tokyo. Tsallan nasa da ya samu gwal ya kafa tarihi da shi na mita 7.17 duk da cewa mako shida kafin gasar ne ya soma atisayen wasan.
Ganin cewa yana da kyakkyawar makoma a wasan, matashin wanda ƙafafuwansa duk an yanke su tun yana da shekara 10 - yake haɗa wannan wasannin da kuma karatunsa.
A watan Afrilu, ya kafa tarihi a duniya inda ya yi gudun mita 200 cikin daƙiƙa 22.94.