Gwarazan ƴan takarar wasanni na BBC Aspoty 2021: Bayani kan Faith Kipyegon
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Faith Kipyegon ta kafa tarihi a Tokyo bayan ta kare kyautar da ta samu ta gudu mai nisan mita 1,500 wanda ta taɓa lashewa a Rio de Janeiro a 2016.
Matashiyar ƴar Kenya ta sadaukar da kyautar da ta samu ga ƴarta mai shekara uku, wadda take ba ƙwarin gwiwa bayan ta ɗauki hutun watanni 21 daga motsa jiki.
Tana daga cikin gwarazan ƴan takarar wasanni shida na BBC Aspoty 2021.