Isa Amadu: Mai tallan ayar da ke 'gogayya' da ma'aikatan banki a Abuja

Bayanan bidiyo, Isa, mai sayar da aya a Abuja
An wallafa

Latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallon Isa mai aya ya zanzare.

Isa wanda dan asalin jihar Kebbi ne ya ce da farko ya fara sana'ar sayar da aya ne da bashi inda idan ya sayar sai ya je ya biya ya sake daukar wata.

Isa dai yana zanzarewa kamar wani ma'aikacin banki sannan ya fita ya tafi tallan ayar da ya saba.

"Na ga ma'aikatan banki suna yin irin wannan shiga a saboda haka na ce idan za su sanya ni mai zai hana ni sanyawa. Shi ne watarana na shiga kasuwar UTC a Abuja na je na sayo." In ji Isa.

Burin Isa dai a yanzu haka shi ne ganin yaransa sun yi karatun boko domin su ci amfani rayuwa duk da cewa shi din bai samu damar yin karatun ba.

Ɗaukar hoto da tacewa: Chukwuemeka Anyikwa

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla: