Maiduguri: Rayuwa a garin da 'yan Boko Haram suka addaba a baya

Bayanan bidiyo, Maiduguri: Rayuwa a garin da 'yan Boko Haram suka addaba a baya
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Bayan shekara 12 da fara rikicin Boko Haram a birnin Maiduguri da kuma kusan durkusar da binin da 'yan Boko Haram suka yi, a yanzu birnin ya farfado, al'amura sun koma kamar yadda suke gabanin Boko Haram.

Cikin shekarun da aka yi ana fama da rikicin Boko Haram, mayakarn sun kai hare-hare marasa iyaka birnin na Maiduguri, inda a nan ne aka yanke kishiyar kungiyar.

Daruruwan mutane sun rasa rayukansu, an rasa dukiya mara iyaka, sannan al'amuran kasuwanci da na zamantakewa sun tsaya, sannan jama'a sun ringa rayuwa cikin fargaba.

To amma a yanzu hankula sun kwanta a cikin birnin, al'amura sun koma kamar a baya, sannan harkokin kasuwanci suna kara kankama.

Sai dai duk sawu na daukewa daga misalin karfe sha daya na dare har zuwa kimanin shida na safe, inda jami'an tsaro ke ci gaba da sintiri a cikin birnin.

Haka kuma ana rufe hanyoyin shiga birnin tun daga karfe shida na yamma har zuwa wayewar gari.