Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Ibrahim Mustapha Malik
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya Malam Ibrahim Mustapha Malik ya ce ya samu karatun addini a ƙasar Saudiyya kuma ya yi karatun boko har zuwa digiri na biyu.
Malamin ya ce yana cikin manyan almajiran Sheikh Abba Aji fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Borno.
Ya ce ya yi karatun litattafai da dama wurin malaminsa Shekih Abba aji.