Matsalar tsaro ba ta hana iyaye tura 'ya'yansu makaranta ba a Borno
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daidaituwar al'amura da kwanciyar hankalin da aka samu a birnin Maiduguri na jihar Borno dake arewacin Najeriya sun sa iyaye cire fargabar tura 'ya'yansu makarantu a cikin birin.
Yawan daliban da suke zuwa makarantun a yanzu sun sa duka makarantun cikin birnin sun cika makil, har ma wasu ajujuwan ba sa isar daliban dake zuwa domin daukar darasi.
A baya dai kungiyar Boko Haram mai yaki da karatun zamani ta sha kai hare-hare makarantu a cikin birnin Maiduguri kamar yadda ake kai hare-haren a wasu sassan birnin.
Gwamnatin jihar Borno ta ce matsalar Boko Haram da ta ilasatawa fiye da mutum miliyan biyu yin kaura zuwa Maiduguri, ta sa makarantun birnin sun yi wa dalibai kadan.
Iyaye sun ce a yanzu ba su da fargabar tura yaransu makaranta, domin al'amura suna daidaita, sannan yanayin da ake ciki ba zai sa su bar yaransu cikin jahilci ba, don haka suna tura su makarantun, tare da addu'o'in neman tsari.