Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Kyari Muhammed
Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Kyari Muhammed, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata sura a Al-Ƙur'ani.
Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC cikin shirin nan mai taken "Ku San Malamanku".
Ya ce surar da ta fi ba shi wuya ita ce Suratul An'am, wadda ita ce sura ta shida daga sama a cikin littafi mai tsarki.
Sai dai ya ce Allah ya sahale masa ayar da ta fi bai wa mafi yawan mahaddatan Kur'ani mai girma wuya, wato ayar rabon gado ta .... Yusi kumullahu, wadda take a cikin Suratul Nisa'i.
Malamin ya ce babu abin da yake faranta masa rai a rayuwa irin ya ga mutum ya musulunta kuma ya yi ruko da addinin yadda ya kamata.
Abin da kuma ya fi bakanta masa rai shi ne "yadda mutane ke wasa da ilimi, yadda ake ba da fatawa bisa kuskure ba tare da damuwa kan abin da zai faru ba".
A lokuta da dama malamai kan yi fatawoyin da suke ingiza mutane su je su rika yi wa shugabanni tawaye ko wani abu mai kama da haka.