Mace mai ƙwallon kwando da ke sauya tunanin mutane a kan mata Musulmai

Bayanan bidiyo, Mace mai ƙwallon kwando da ke sauya tunanin mutane a kan mata Musulmai
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Miliyoyin mutane ne suke kallon bidiyon da Jamad Fiin ke yi na wasan ƙwallon kwando.

Kwalejin wasan ƙwallon kwando da ke Boston a Amurka, tana amfani da wasannin matar don ƙarfafa wa matasa gwiwa.

Jamad Musulma ce kuma wasan kwandon da take yi ya ja hankalin mutane da dama a faɗin duniya da sanya wa su sauya tunaninsu a kan irin kallon da a baya suke yi wa mata Musulmai.