Dalilin da ya sa nake yi wa Buhari waka - Rarara
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya Dauda Adamu Kahutu Rarara ya ce gaskiyar Buhari ce ya sa yake yi wa shugaban na Najeriya waka.
Rarara ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi ta musamman da BBC, inda yake cewa tun yana yaro ake nusantar da shi kan gaskiya da amanar Buhari kuma har yanzu da ya taso ya gani.
Dauda ya kara da cewa burin da Buhari yake da shi na gyara Najeriya da ayyukan da yake yi a yanzu ba za su kirgu ba.
Ko da yake a yanzu ya ce yana dab da sakin wasu wakoki da za su bayyana irin ayyukan da Shugaba Buhari yake yi da wadanda ya kammala, wanda a cewarsa "mutane za su gamsu da ceton Najeriya da Buhari ke yunkurin yi."
Rarara wanda ya karɓi kuɗin wasu ƴan Najeriya don rera wa Buhari waƙa, kuma har yanzu bai saki waƙar ba, ya ce idan da ƴan Najeriya za su karɓi ra'ayinsa da sun bari gwanin nasa ya zarce ya ƙara shekara biyar kan mulki - "don ya kammala ayyukan da ya fara."
Mawaƙin siyasar ya ce ba daɗewa ba zai saki wasu waƙoƙi guda uku kan ayyukan Buhari.
Sai dai bai bayyana lokacin da zai saki waƙoƙin ba, ciki har da wadda ya kira mai taken "shidan Buhari ta fi sha shidan gangan"