Rabi'u Kwankwaso: Tsohon gwamnan Kano ya ce bai yi mamakin rikicin APC a Kano ba

Bayanan bidiyo, Rabi'u Kwankwaso: Tsohon gwamnan Kano ya ce bai yi mamakin rikicin APC a Kano ba
An wallafa

Latsa hoton da ke sama ku kalli bidiyo:

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ɗora alhakin rikicin da jam'iyyar APC a jihar Kano ta faɗa kan abun da ya kira ''Son rai, irin na gwamnan jihar mai ci Abdullahi Umar Ganduje''.

Yayin wata hira da sashen Hausa na BBC, Kwankwaso ya ce ko kaɗan bai yi mamakin rashin jituwar da ta dabaibaye jam'iyyar da ke jagoanci a jihar Kano ba, tuntuni ya san haka za ta faru, batu ne kawai na lokaci.

''Duk wanda yake ba zai iya rike wanda ya masa alheri shekara da shekaru ba, wanda shi ma da kansa yana fada cewa na masa, amma shi randa ya samu dama rana daya tak ya kasa iya rike Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya, to kaga ai ba zaman lafiya'' inji Kwankwaso.

Sanata Kwankwaso, ya ce ba bu abun da ya yi tasiri a rikicin jam'iyyar ta APC a Kano face tsagwaron son rai da son zuciya, da kuma rashin haƙuri. ''Ni abun ya ma sake tabbatar min da abun da nake zato ne kawai'' inji shi.

Ya kara da cewa dama Hausawa kan ce ƙarya fure kawai take ba ta 'ƴa'ƴa, don haka ga shi lokacin da ake jira ya zo.