BBC Africa Eye: Ko biyan kuɗin fansa zai ƙara jefa ɗaliban Najeriya cikin hatsari?
An wallafa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon:
Dubban ɗalibai da malamai ne aka yi garkuwa da su a arewacin Najeriya.
Yawan sace-sacen babban ƙalubale ne ga ƙasar, wadda ta fi yawan yaran da ba su zuwa makaranta a duniya.
Ana tursasawa iyayen yara biyan maƙudan kuɗi domin ƴancin 'ƴa'ƴansu, kuma yawan iyaye yanzu na tsora da tura 'ƴa'ƴansu makaranta.
Mayeni Jones, ta kai ziyara arewa maso yammacin Najeriya inda ta gana da waɗanda abin ya shafa da kuma abin da ƙe ƙara rura wutar matsalar.