Yadda dala ke ci gaba da murkushe darajar naira a Najeriya

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Yadda dala ke ci gaba da murkushe darajar naira a Najeriya
An wallafa

Ku latsa sama don kallon bidiyon:

Darajar kudin Najeriya naira na ci gaba da faudwa warwas.

Yanzu maganar da ake takardar kudin CFA da ake kashewa a wasu kasashen Afrika kamar Nijar, Kamaru da Chadi, darajarta ta kamo ta naira.

Wato sai ka ba da naira 1000, za ka canja wannan saifa dubu daya.

Idan kuna shirin zuwa Umrah, to ‘yan canji za su siyar muku da Riyal a kan naira 140 kowacce riyal daya.

A shekarar 2015 ana musayar dala daya a kan naira 200 da motsi a kasuwar bayan fage.

Sannan a farkon shekarun 1980, ina nufin kimanin shekara 41 da suka wuce, naira ta fi dala daraja.