Ko kun san bashin da ake bin ku a matsayinku na 'yan Najeriya?

Bayanan bidiyo, Yawan bashin da ake bin Najeriya
An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na Najeriya ya nemi majalisa ta ba shi dama ya ranto bashin kusan Tiriliyan biyu.

Shugaban na neman damar rancen ne domin domin cike gibin kasafin kudin kasar na shekarar 2021.

A Maris din 2021 ne Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya DMO bayyana cewa bashin da ake bin kasar ya kai naira tiriliyan 32.915 daga ƙarshen watan Disamban 2020.

Ofishin ya ce sabon bashin da Shugaba Muhammadu Buhari zai karɓo zai sa bashin da ake bin kasar ya kai naira tiriliyan 36.3.