Bidiyon kantin sayar da malafa mafi dadewa a duniya

Bayanan bidiyo, Bidiyon kantin sayar da malafa mafi dadewa a duniya
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An bude kamfanin Lock & Co a 1676 a St James's da ke tsakiyar birnin London, kuma ana kallonsa a matsayin kantin sayar da malafa mafi dadewa a duniya.

Fitattun mutanen da suka sayi malafa a kantin sun hada da Duke na Wellington, Winston Churchill, da kuma Charlie Chaplin.

Kantin ya ci gaba da kasuwanci duk da kalubalen da ya fuskanta a lokacin yakin duniya na Daya da na Biyu, da lokacin matsalar karyewar tattalin arzikin duniya.

Sai dai kuma ta yaya yake ci gaba da fuskantar kalubalen da annobar korona ta bijiro da su?