Taliban: Sojan Amurka na ƙarshe da ya fita daga Afghanistan
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Jirgin sojin Amurka na ƙarshe ya bar filin jiragen sama na Kabul a ranar Talata, 31 ga watan Agusta 2021.
Hakan ya kawo ƙarshen shekara 20 ɗin da Amurkar ta shafe a Afghanistan.
Tafiyar jirgin ya kawo ƙarshen babin zaman dakarun Amurka da ke yaƙi da Taliban a ƙasar, inda ficewar Amurkar ya jawo sake ƙwace mulki da Taliban ta yi da ƙasar tun bayan shekarar 2001.