Mahaifina ne ya tsaya min a waƙa - DJ AB

Bayanan bidiyo, Mahaifina ne ya tsaya min a waƙa - DJ AB
An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Matashin mawaki Haruna Abdullahi wanda aka fi sani da DJ AB ya ce ya fuskanci ƙalunbale kafin ya samu karɓuwa musamman ga matasan arewacin Najeriya.

A hirarsa da BBC ya ce ya samu goyon bayan mahaifinsa, wanda ya fara sayo masa abin ƙida na piano.

Ya ce yanzu ya samu ɗaukaka, kuma yana alfahari da ɗimbin masoyansa.

“Da sai mun biya muke waka yanzu kuma sai an biya mu idan za mu yi waƙa,” in ji mawaƙi DJ AB.

DJ AB ɗan asalin jihar Kaduna ne. Kuma yi karatun shi na furamare da sakandare a jihar ta Kaduna.

A halin yanzu yana karatun digirinsa na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke garin Zaria.

Matashin ya kuma ce yana sha’awar abinci amma wanda aka lulluɓe da nama.

Wasu ƙarin bidiyo da za ku so ku kalla