Ranar Hoto Ta Duniya: Yadda zaku samu kudi daga daukar hoto

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Yadda zaku samu kudi daga daukar hoto
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An ware ranar sha tara ga watan Agustan ko wace shekara a matsayin ranar hoto ta duniya.

An kebe ranar ce domin nazari kan irin gudunmawar da hoto ke bayarwa a fannoni daban-daban na tarihi da rayuwar dan Adam da dabbobi da kuma sauran abubuwa.

BBC ta tayi hira da wani fitaccen mai daukan hoto a Najeriya Habila Mazaje.

Ya kuma bayyana irin muhimmanci da hoto ke da shi ga bangarorin rayuwa daban-daban.

Ɗaukar bidiyo: Bashir Idris

Tsarawa da gabatarwa: Salihu Adamu Usman