Yadda takari suka cashe a Kano da al'adun Saudiyya

Bayanan bidiyo, Yadda takari suka cashe a Kano da al'adun Saudiyya
An wallafa

Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:

Hausawa kan ce kowa ya bar gida, gida ya bar shi, amma kuma akan ce gida biyu maganin gobara.

Abin da ke faruwa ke nan ga wasu al’ummar Hausawa wadanda suka shafe wani bangare na rayuwarsu a kasar Saudiyya tare da Larabawa. Inda aka samu cakuduwa tsakanin al'adar Hausa da ta Larabawa.

Yanzu haka wasu daga cikin irin wadannan mutane da suka dawo gida sun ce suna kewar al'adun da suka baro a kasar ta Saudiyya duk da cewa ba su da niyyar komawa can da zama.

Wadannan mutane kan ware wani lokaci a duk shekara domin tunawa da irin al'adun da suka baro, abinda suka yi wa lakabi da "Muzmar'.

A wannan shekarar ma sun hada irin wannan biki a gidan zoo da ke Kano, wanda ya zo daidai da lokacin da shugabansu ke angwancewa.