Daga Bakin Mai Ita Tare da Malam Tsalha na Dadin Kowa
An wallafa
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 60, shirin ya tattauna da Ahmad Isma’il Basso, wanda aka fi sani da Malam Tsalha, da ke fitowa a shirin talbijin na Daɗin Kowa.
A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da rawar da yake takawa a shirin.
Ɗaukar bidiyo da tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir
Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh