Bayani kan shekara 12 da kafa shafin BBC Hausa Facebook
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ranar 4 ga watan Agustan 2009 ne aka bue shafin BBC Hausa Facebook, kuma a yanzu ya cika shekara 12 kenan.
hafin Facebook na BBC Hausa ya cika shekara 12 da kafuwa a ranar 4 ga watan Agustan 2021.
Shafin na daya daga cikin hanyoyi daban-daban na zamani da BBC Hausa ke amfani da su wurin isar da labarai ga mabiyanta musamman matasa.
Mutum sama da miliyan hudu ne ke samun labarai ta wannan kafa da BBC Hausa ta samar shekaru 12 da suka wuce.
Shugaban Sashen wanda aka kuma buɗe shafin tare da shi, wato Aliyu Tanko, ya yi bayani yadda abin ya kasance.