Dadiyata: shekara biyu kenan tun bayan sace wani matashi a gidansa a Kaduna

Bayanan bidiyo, Shekara biyu da sace Dadiyata babu amo babu labari
An wallafa

Shekara biyu kenan a yau 2 ga watan Agusta tun da aka sace Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata a gidansa a Kaduna.

Matashin wanda ya yi fice a tafiyar Kwankwasiyya da kuma sukar gwamnati ya yi batan dabo har yanzu babu wanda ya gan shi ko kuma ya san inda yake.

A wannan hira ta musamman da BBC ta y da mahaifansa da matarsa da kuma kawunsa wanda sanadin samun labarin sace Dadiyata jikinsa ya shanye, sun bayyana mana irin halin da suke ciki.