Ahmed Gambo Salman Ahmerdy: Abin da ya sa na yi wa mata wakar 'kallabi'

Bayanan bidiyo, Abin da ya sa na yi mata wakar 'kallabi' - Ahmerdy
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Matashin mawakin nan da ya yi fice da wakarsa mai suna 'kallabi', Ahmed Gambo Salman wanda aka fi sani da Ahmerdy, ya ce ya sauke Alku'rani sau biyu.

A wata tattaunawa da BBC Hausa, Ahmerdy ya ce ya rera wakar 'kallabi' ce domin ya karfafa wa mata gwiwa su rika sanya dankwali.

Matashin mawakin, dan asalin jihar Kano da ke arewacin Najeriya wanda yanzu haka yake karatun Digiri a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha da ke Wudil, ya ce ya fara waka a 2019.