BBC Africa Eye: Yadda 'rashawa' ke sa masu ikirarin jihadi samun nasara kan sojojin Mali

Bayanan bidiyo, Zargin rashawa da cin hanci a tsakanin sojin Mali
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

Kasar Mali da ke yankin Afirka ta Yamma na fama da hare-haren masu ikirarin jihadi kimanin shekaru tara da suka gabata.

Sojojin kasar na rasa rayukansu sakamakon shekarun da suka kwashe suna yaki da wadannan masu tayar da kayar baya ne, inda iyalai da dama suka zama marayu.

Ana alakanta rashawa da cin hanci da babban dalilin da ke janyo mayakan ke yin nasara a kan sojoji inda ake saya wa sojojin kayayyakin yaki marasa inganci kamar rigar sulke.

BBC ta nemi jin ra'ayin hukumar soji kan zarge-zargen rashawa da cin hanci amma ba su ce uffan ba.

Wasu bidiyon masu alaka da za ku so ku kalla