Bidiyon yadda ambaliyar ruwa ke gudu da mutane a China
An wallafa
Ku latsa hoton sama don kallon bidiyon:
Shugaban China XI Jinping ya bayyana ambaliyar ruwa da ake yi a lardin Henan na tsakiyar kasar a matsayin mai matuƙar muni kuma an shiga mawuyacin hali.
Ambaliyar na faruwa ne sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin masaki.
Cikin hotunan bidiyo masu ban al'ajabi, an ga fasinjoji cikin jiragen ƙarƙashin ƙasa wadanda ruwa ya malale a babban birnin lardin wato Zhenghou inda aka tabbatar da mutuwar mutum 12 kawo yanzu.
A wasu hotunan bidiyon kuma an ga ruwa mai ƙarfi na yin awon gaba da motoci da mutane a tituna.