Matar da mijinta ya harbe ta a fuska a Afghanistan

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Matar da mijinta da harbe ta a fuska a Afghanistan
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Afghanistan na daya daga cikin kasashe mafi muni ga mace ta yi rayuwa a can.

A bara kawai an ci zarafin kusan mata 3,500 kuma ana fargabar yawan zai karu saboda yadda sha’anin tsaro ke sake lalacewa.

Shakila Zareen mai shekara 25, na daga cikin mata kalilan da ta tsallake siradi bayan da aka yi mata tiyata har sau 22 bayan da mijinta ya harbe ta.