Hajj 2021: Falalar goman farko na watan Dhul Hijja na Babbar Sallah
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Sheikh Muhammad
Watan Dhul Hajji shi ne wata na 12 a tsarin kwanan wata na Musulunci kuma a watan ne ake yin tsaiwar Arafat da sallar Idi.
Malamai na jan hankalin Musulmi da su dage da neman rabauta a wannan wata kama daga yawan ibada da sadaka da kyauta da kuma yawan ambaton Allah da annabinsa.
Sheikh Muhammad Mashhud ya ce "ana son mutum ya dage da yawan karatun al'qur'ani da salatin annabi da yawaita azumi da kyautatawa jama'a."
Watan na Dhul Hijja dai na daya daga cikin watanni guda hudu da Allah ubangiji ya kira da 'Arba'tu Hurum.'