Bidiyon garken tumakin da ya ja hankalin mutane a Isra'ila

Bayanan bidiyo, Bidiyon garken tumakin da ya ja hankalin duniya
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani mai ɗaukar hoto ɗan Isra'ila ya yi fice bayan da wani bidiyon garken tumaki da ya ɗauka ya yaɗu kamar wutar daji.

An kalli bidiyon sau fiye da 100,000 a Facebook.

Lior Patel da ya ɗauki bidiyon da jirgi maras matuƙi, ɗan Haifa ne daga Isra'ila, ya kuma shaida wa BBC yadda ya ji kan yaɗuwar bidiyon.