Mohamat Idriss Deby: Kalaman shugaban kan yiwuwar tsawaita mulkinsa sun tayar da kura a Chadi

An wallafa

Jam'iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula a Chadi har ma da limaman addinai na mayar da martani a kan wasu kalamai da shugaban riƙo Janar Mohamat Idriss Deby ya yi cewa gwamnatinsu na iya tsawaita wa'adin mulkinta.

An kuma ambato Mohamat Idriss na cewa Chadi ba ta da kuɗin gudanar da zaɓuka cikin ƙasa da shekara ɗaya da rabi.

'Yan adawan ƙasar dai sun yi kira ga gwamnati da shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar su yi hattara kada tarihi ya maimaita kansa.

Sanusi Mukhtar, wani ɗan jarida a Njamena babban birnin Chadi ya yi wa BBC karin bayani kan abin da kundin mulkin riƙon ƙwaryar ya tanada.

Ya ce kundin ya yi tanadin cewa sojojin da suka kwace mulki za su jagoranci ƙasar tsawon wata 18 bayan nan kuma sai a shirya zabe.

Ya kara da cewa a karkashin kundin, za a iya sabunta wa'adin na wata 18 sannan za a iya gyara kundin ta yadda za a iya ci gaba da mulki.

A cewarsa, babu wani waje cikin kundin da aka hana shugaban rikon tsayawa takara - "ba inda aka ce kar ya tsaya, tun da ba a ce kar ya tsaya ba ke nan zai iya tsayawa a karkashin wannan kundin". in ji dan jaridar.

Tun da farko a cewar dan jaridar, Mohamat Idriss Derby ya gindaya wasu sharuda na mika mulki bayan cikar wa'adinsu na wata 18.

"Ka'ida daya ita ce yan Chadi su sasanta da junansu su yafewa junansu su amince da junansu,

"Na biyu sai idan hukumomi na kasa da kasa sun taimaka musu da kudi saboda a yanzu ba su da kudin da za su shirya zabe a wannan wa'adi na watanni 18". in ji Sanusi Mukhtar.