Salihu Usman Zurmi Gurgu: Ɗan majalisar jihar Zamfara ɗaya tilo da ya ƙi komawa APC
An wallafa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Ɗan majalisar Zamfara ɗaya tilo wanda ya ƙi bin gwamna da sauran ƴan majalisar jihar zuwa APC ya ce baya ga akida, ficewa jam’iyyar PDP kamar yin butulci ne ga ni’imar da Allah Ya yi masa.
Honarabul Salihu Usman Zurmi Gurgu, dan majalisa mai wakiltar Zurmi ta gabas ya ce ba ya tsoron zama ɗan adawa a majalisar jihar ta Zamfara.
"Ba zan butulce wa ni'imar da Allah ya min ba sanadin PDP," in ji Ɗan majalisar