Aminu Ado Bayero: Yadda aka yi bikin ba Sarkin Kano sandar girma
An wallafa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Gwamnan Kano Umar abdullahi Ganduje ya gabatar da sandar gima ga Sarkin Kano Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero bayan shekara ɗaya kan gadon sarautar Kano
Bikin bayar da sandar da aka yi a filin wasa na Sani Abacha a Kano a ranar Asabar ya samu halartar sarakuna na ciki da wajen Najeriya.
Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnonin APC da manyan ƴan siyasa a Najeriya na cikin waɗanda suka halarci bikin.