Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malama Murjanatu Ibrahin Kaita

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malama Murjanatu Ibrahin Kaita
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A wannan makon shirin Ku San Malamanku ya tattauna ne da Malama Murjanatu Ibrahin Kaita daga jihar Katsina.

Malama ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha wajen neman ilmi kafin Allah ya kai ta ga samun nasarar kai wa ga matakin karatun da take kai a yanzu.

Ta kuma ce tana da burin yin amfani da karatun da ta yi wajen fadakarwa, da koyar da al'umma, musamman mata a bisa tafarkin addinin Musulunci.