Umar Kasagi: An karrama gwamnatin Najeriya kan littafina Kulba na Barna, amma gwamnati ba ta karrama ni ba
Latsa wannan hoton na sama domin kallon Umar Danjuma Katsina
Fitaccen dan wasan kwaikwayon nan na arewacin Najeriya, Umaru Danjuma Katsina wanda aka fi sani da Kasagi ya ce a zamaninsu "a kan samu yanayin da surukai kan iya zama su kalli wasan kwaikwayo tare saboda babu wani abin da za a nuna wanda bai dace ba."
Kasagi ya fito a wasannin kwaikwayo a shekarun 1980 - irin su Magana Jari da Kasagi da Karambana da Tambari da dai sauransu.
Umaru Kasagi ya taka rawa tare da fitattun 'yan wasan wancan zamani irin su Kasimu Yero da Tumbuleke.
"A wancan lokaci mu ba kudi muke nema ba. Mun yi suna sannan kuma mun kare kimar addini da al'adarmu".
Babban aikin da Malam Umaru Danjuma Kasagi ya yi shi ne littafin 'Kulba na Barna' wanda aka mayar da shi wasan kwaikwayo, wani abu da ya janyo wa Najeriya karramawa.
To sai dai abin da a yau yake ci wa fitaccen dan wasan kwaikwayon tuwo a kwarya shi ne, "an karrama gwamnatin tarayyar Najeriya sakamakon wannan littafi na Kulba na Barna, amma har yau din nan gwamnatin ba ta karrama ni ba."