Ba mu yanke hukunci kan wanda zai shugabanci APC ba - Mai Mala Buni

Bayanan bidiyo, Hirar BBC da Gwamna Mai Mala Buni
An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

A wannan makon ne aka karawa kwamitin riko na jam'iyyar APC karkashin gwamnan jihar Yobe Malam Mai Mala Buni wa'adi domin su kammala aikin da suka fara gabanin zabukan cikin gida.

Shugaban na rikon Mai Mala Buni ya shaida wa BBC irin ayyukan da suka gabatar kawo yanzu, da kuma abin da suka sa gaba.

Haka kuma shugaban na APC ya yi tsokaci kan rade-radin cewa gwamnan jihar Zamfara zai sauya sheka daga PDP zuwa APC a cikin wannan makon.