Bidiyon yadda aka yi wa Yusuf Buhari da ƴar sarkin Bichi baiko

Bayanan bidiyo, Yadda aka yi wa ƴar sarkin Bichi baiko da Yusuf Buhari
An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ba Yusuf Buhari, ɗan Shugaba Buhari na Najeriya, auren 'yar Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, ranar Lahadi.

Tawagar wakilai da ta ƙunshi gwamnoni da manyan jami'an gwamnati tarayya ta nema wa Yusuf auren Zarah Nasir Ado ne a hannun sarkin Kano, wanda yaya ne ga sarkin na Bichi.

Wakilan da suka yi wa ɗan shugaban ƙasar walicci ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu sun haɗa da Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar da Ministan Shari'a Abubakar Malami.

Sauran su ne Gwamnan Borno Babagana Zulum, da tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, da Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna.

Daga bisani tawagar ta je garin Bichi domin gaishe da Sarki Nasiru Ado Bayero.

Wata majiya ta shaida wa BBC Hausa cewa tambayar auren kawai suka je yi, wanda kuma Sarkin Kano Aminu Ado ya ba su, saɓanin rahotannin da ke cewa ɗaura auren aka yi.

Yusuf Buhari da ƴar sakrin Bichi

Asalin hoton, Other

Wasu majiyoyi sun ce matasan biyu sun haɗu da juna a Ingila yayin da suke karatu a can.

Yusuf ne ɗan Aisha Buhari na uku da zai yi aure tun da Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.

Daukan bidiyo: Bappancey_photography