Bidiyon yadda ziyarar Shugaba Buhari zuwa Borno ta kasance

Bayanan bidiyo, Bidiyon yaada ziyarar Shugaba Buhari zuwa Borno ta kasance
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis.

Shugaban na Najeriya ya isa filin jirgin saman Maiduguri da safiyar ranar ta Alhamis kuma daga nan ya shiga aiwatar da abubuwan da suka kai shi jihar.

Wata sanarwa da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Isa Gusau ta ce Shugaba Buhari ya bayyana cewa 'na yi matukar jin dadi' bayan da ya kaddamar da ayyuka bakwai cikin ayyuka 556 da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Shugaba Buhari ya yi tsokaci na musamman kan Makarantar Koyon Ayyukan Hannu da ya kaddamar a Muna, wadda ya bayyana a matsayin wata cibiya da za ta samar da ayyukan yi da kuma rage zaman kashe wando ga matasa ta yadda zai yi wahala kungiyar Boko Haram ta dauke su, a cewar Isa Gusau.