Ku San Malamanku tare da Sheikh Jalo Jalingo
An wallafa
Latsa hoton sama ku kalli bidiyo
Shahararren malamin Musuluncin nan, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Muhammad Jalingo ya ce ya fara karatu ne domin ya ƙware a harshen Larabci da kuma adabi ba wai karatun Fiƙihu da sauransu ba kafin daga baya ƙaddara ta sauya masa layi.
An haifi malamin a garin Jacci da ke Jihar Taraba a arewa ta tsakiyar Najeriya a shekarar 1960.