Mai tallan goron da ke son zama ma'aikacin banki
Ku latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallon hirar
Zubairu Ibrahim wanda dan asalin karamar hukumar Kauru ne da ke jihar Kaduna ya ciri tuta wajen kambama karamar sana'ar da yake yi ta tallan goro da alewa.
Matashin dan shekara 24 yana daukar goron ne da alawa a faranti ya kuma yi masa kantafi inda yake zarya a tsakanin motoci a unguwar Nyanya da ke Abuja.
Zubairu ya kasance mai kiwo da noma lokacin da yake karami kuma tare da mahaifansa.
Burin Zubairu tun yana karami shi ne ya zamo ma'aikacin banki. To sai dai sakamakon rashin samun damar yin karatun boko bai iya cimma mafarkinsa ba.
"Shi ya sa nake kwat a matsayina na mai tallan goro saboda burina na yin aikin banki da zai sa na rinka irin wannan shigar bai tabbata ba."
To sai dai har yanzu Zubairu bai cire ran samun aikin banki ba idan da zai samu gatan yin karatun boko.